
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya mutu.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Akeredolu ya mutu ne da safiyar ranar Laraba yana da shekaru 67. An rawaito cewa gwamnan ya mutu sanadiyar cutar sankarar mafitsara da kuma ta jini.
Wasu majiyoyi a gidan gwamnatin jihar sun tabbatarwa da jaridar The Cable mutuwar gwamnan.
A ranar 7 ga watan Satumba ne gwamnan ya dawo daga jinyar tsawon watanni uku a kasar Jamus inda ya mayar da ofishinsa birnin Ibadan na jihar Oyo
Rashin mika mulki ga mataimakinsa ya haifar da rikicin siyasa a jihar har ta kai ga majalisar dokokin jihar tayi barazanar tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedetiwa.
Biyo bayan tsoma bakin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu majalisar dokokin jihar ta janye batun tsige mataimakin gwamnan kana shima mataimakin gwamnan ya janye karar da ya shigar gaban kotu domin ta hana majalisar dokokin jihar tsige shi.
A ranar 12 ga watan Disamba ne gwamnan ya sanar da cewa zai sake tafiya hutun jinya kuma ya mika ragamar jagorancin jihar ga mataimakin gwamnan jihar.