Gwamna Zulum Ya Umurci Biyan Ma’aikatan Jihar Borno Albashinsu

VOA Hausa

Gwamna jihar Borno Babagana Umar Zulum, ya bada umurnin biyan dukkannin ma’aikatan jihar da basu samu albashin su ba sakamakon wani aikin tantancewa da gwamnatin jihar Borno ta soma tun shekaru hudu da suka gabata domin tantace ma’aikata da ‘yan fashon jihar.wanda hakan ya haifar da rashin samun albashin wasu ma’aikata tare da wasu yan fanshon fashon.

A baya baya ne kungiyar tsofofin yan fashon suka gudanar da zanga zangar rashin samun hakkokin su, A halin yanzu gwamna Zulum ya dakatar da wannan tantacenwar domin a biya ma’aikatan albashin su inda yanzu haka akwai mutane kimanin 296 da ba’a biya su albashinsu ba duk da cewa an kammala aikin tantacen su.

Don haka ne, Gwamna Babagaba Umar Zulum ya umarci jihar da ta biya albashi da gaggawa. Ya kara da cwa, duk wani ma’aikacin da aka kama da laifin almundahana za’a hukunta shi domin kuwa ana samun ma’aikata da suke ansar albashi fiya da daya.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...