Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya kaddamar da wani shiri na musamman don tallafa wa karatun yara mata a duk faɗin jihar, a wani yunƙuri na rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Shirin, wanda aka yi wa take da “Adolescent Girls’ Initiative for Learning and Empowerment” (AGILE), na nufin inganta damar da mata yara za su samu na ilimi, tare da ƙarfafa ayyukan koyo da koyarwa a jihar Sokoto.
A cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafin Facebook ɗinsa, ya bayyana cewa, ƙarƙashin wannan shiri, makarantun sakandare na mata guda 240 za su amfana da tallafin kuɗaɗe domin inganta ilimi a tsakanin su.
Gwamna Ahmad Aliyu Ya Kaddamar da Shirin Tallafa Wa Karatun Yara Mata a Sokoto
