Gwamanti da ‘yan adawa sun cimma sabuwar yarjejeniya game da rikicin Sudan

Sudanese people celebrate in the streets of Khartoum after ruling generals and protest leaders announced they had reached an agreement on the disputed issue of a new governing body on 5 July

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A watan jiya ‘yan Sudan sun fita bisa tituna suna nuna farin cikinsu kan waccan yarjejeniyar raba mukamai da aka kulla

Majalisar sojoji da ke mulkin Sudan da babbar kungiyar fararen hula masu zanga-zanga a kasar sun cimma yarjejeniya kan sabon wa’adin gwamnatin rikon kwarya da za a kafa a kasar.

Kasar Sudan na cikin rikicin siyasa tun bayan da sojoji suka hambare tshon Shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilu.

Jakadan Kungiyar Kasashen Afirka, AU, Mohamed Hassan Lebatt ne ya sanar da cima yarjejeniyar da sanyin safiyar yau Asabar amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Mista Lebatt ya bayyana wa manema labarai cewa: “Ina sanar da ‘yan kasar Sudan da ‘yan Afirka da sauran mutanen duniya cewa wakilan bangarorin biyu sun amince da yarjejeniyar a hukumance.”

Ya kuma ce akwai sauran aiki da za a yi kafin a fayyace sauran abubuwa, gabanin rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar, amma bai bayar da cikakken bayani ba.

An dai shafe watanni ana tattaunawa tsakanin gwamnatin mulkin soji ta kasar da kungiyoyin fararen hula a daidai lokacin da tashin hankali ke neman jefa kasar cikin yakin basasa.

A watannin baya, gwamnatin ta Sudan da masu adawa da ita sun cimma yarjejeniya kan batutuwa masu yawa, amma da zarar an kusa rattaba hannu kan yarjeniyoyin, sai wani bangare ya fito da wasu sabbin bukatu.

Daftarin yarjejeniyar da aka amince da shi a watan jiya ya fayyace cewa za kafa wata sabuwar gwamnati da fararen hula shida da janar-janar na sojojin kasar biyar.

  • Sudan na neman kara rincabewa
  • Ana gudanar da sabuwar zaga-zanga a Sudan

Me daftarin yarjejeniyar ya kunsa?

Tuni dai aka cimma wata matsaya game da raba mukamai tsakanin bangarorin biyu, kuma bangarorin sun amince da yawancin mataka da aka bayyana.

Na farko shi ne za a gudanar da mulkin karba karba na wata 39, kafin a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar kasar.

Za a nada firai minista wanda bangare masu zanga-zanga ne za su nada, kuma shi ne zai jagoranci majalisar ministocin kasar.

Amma sojoji ne za su nada ministan tsaro da na harkokin cikin gida.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...