
Gidaje da dama,motoci da kuma dukiya ta miliyoyin Naira ne suka lalace bayan da wata tankar mai ta kama da wuta a garin Lambatta dake jihar Niger.
Tankar dake makare da man fetur ta yi bindiga tare da kamawa da wuta bayan da tayi arangama da wata motar tirela.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe n 11 na daren ranar Lahadi inda gidaje da dama suka kone kafin zuwan jami’an hukumar kashe gobara daga Suleja.
Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa ta alakanta faruwar hadarin a dalilin kwacewar da daya daga cikin motocin tayi.