‘Gobara ta lalata dukiyar naira tiriliyan uku a Najeriya’

Gobara ta lalata dukiyar da ta kai ta naira biliyan dubu 3, wato tiriliyan 3 a Najeriya, kamar yadda Ministan harkokijn cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola ya bayyana.

Ministan ya ce kasar ta tafka wannan asara ne a sanadiyyar gobara 2,845 da aka samu a sassan kasar daban-daban a shekarar da ta wuce, 2021.

Aregbesola

Aregbesola ya sanar da haka ne jiya Laraba yayin da yake sanya lambobin karin girma ga manyan shugabannin hukumar kashe gobara ta tarayyar kasar, a Abuja.

Ministan ya kuma ce hukumar ‘yan kwana-kwana ta yi nasarar kare kadarar da ta kai ta naira tiriliyan 18.9 trillion da ceto mutane 260 daga gobara.

Ministan, wanda ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa tare da kai dauki na kashe gobara har 2,845 a shekarar da ta wuce 2021, y ace sun samu wannan nasara ne saboda a tsakanin 2015 zuwa yanzu hukumar ta samu kayan aiki fiye da yadda take samu tun lokacin da aka kirkiro ta a 1991.

More from this stream

Recomended