Gebrselassie ya zargi Facebook da haddasa rikicin Habasha | BBC news

Hakkin mallakar hoto
Reuters
Image caption

Matasan Oromo rike da makamai a Habasha

Fitaccen dan gudun famfalaki na kasar Habasha Haile Gebrselassie ya damu kan yadda labaran karya da ake yadawa a Facebook ke taimakawa wajen rura wutar rikicin kabilanci.

Zakaran na Olympic ya shaida wa BBC cewa labaran kanzo kurege da ake yadawa a Facebook sun taka rawa a rikicin da ya faru a yankin Oromia wanda ya janyo hararar rayuka 78.

Ya ce kada Habasha mai mutum miliyan dari, ya kamata a yi taka-tsan tsan, abin da ya faru Rwanda ba a dade ba da rikice-rikice a Syria da Yemen da Libya.

“Tabbas Firaministanmu yana kokarin tabbatar da zaman lafiya amma dole sai an yi aiki tare da kamfani kamar Facebook wajen tabbatar da zaman lafiya.”

Ya ce yadda ake yada kalaman karya a Facebook na tattare da hatsari ga tsaron kasa.

Dan tseren gudun wanda yanzu babban dan kasuwa ne a Habasha ya yi kira ga Facebook ya taimaka ya dinga toshe kalaman karya da kan iya haifar da rikicin kabilanci da na addini.

Ko da yake ba za iya gane tasirin da kafafen sada zumunta na intanet kamar Facebook suka yi ba wajen rura wutar rikicin na watan da ya gabata, amma wasu kalaman da aka yada a Facebook suna da hatsari, musamman na karya da aka yada inda aka zargi dan sanda yana ba matasa makamai.

Rikicin Oromia ya samo asali ne bayan wani mai kamfanin jarida Jawar Mohammed ya zargi hukumomi da yi wa rayuwarsa barazana bayan janye masu gadinsa.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...