Ganduje Ya Nemi Kotu Ta Hana EFCC Binciken Bidiyon Dala

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nemi wata babbar kotu a jihar da ta hana hukumar EFCC binciken sa har abada akan bidiyon da aka fitar yana saka daloli a aljihun babbar riga.

A shekarar 2018 ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa bidiyon da ya nuna Ganduje ya na karɓar cin hancin dala daga wani ɗan kwangila.

A lokacin gwamnan ya ƙaryata bidiyon inda ya ce ƙirƙirar sa aka yi.

Tsohon Antoni Janar na jihar shi ne ya shigar da karar inda ya nemi kotun da ta hana hukumar EFCC binciken sa har sai an kammala shari’ar dake gaban kotu tsakanin Ganduje da Ja’afar Ja’afar mamallakin jaridar ta Daily Nigerian.

Ganduje ta hannun lauyan nasa ya nemi kotun da ta ayyana cewa gayyatowa tare yin tambayoyi ga tsohon shugaban hukumar SUBEB da kuma Akanta Janar na jihar ya saÉ“a wa ka’ida.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...