FIFA da NFF sun ƙaddamar da ƙaramin filin wasa a jihar Kebbi

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA da kuma hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF sun ƙaddamar da wani f ƙaramin filin wasa a jihar Kebbi.

A ƙalla dalar Amurka miliyan 1.19 aka kashe wajen samar da filin wasan.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN gwamnan jihar, Nasir Idris shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da filin wasan dake kan titin Kalgo a birnin Kebbi.

A cikin watan Satumba na shekarar 2020 tsohon gwamnan jihar,Atiku Bagudu ya aza harsashin ginin filin wasan.

Da yake magana a wurin bikin shugaban hukumar NFF, Ibrahim Gusau ya ce hukumar za ta cigaba da samar da sauran kayayyaki a filin domin daga darajarsa a nan gaba.

More from this stream

Recomended