
Shugaban kasa, Muhammad Buhari a ranar Alhamis ya gana da gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.
Wannan ne karo na farko da Buhari da Emefiele suke ganawa a cikin shekarar 2023.
A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN mutanen biyu sun gana har sau biyu a fadar Aso Rock dake Abuja a yau.
Tun da farko Emefiele ya halarci fadar shugaban kasa tare da tawagar Bankin Samar da Cigaba na Kasashen Labarawa da suka kai wa Buhari ziyara.
Daga baya ya koma fadar da misalin karfe 02:40 na rana inda suka yi ganawar sirri da Buhari ta tsawon minti 25.
Amma kuma gwamnan babban bankin yaki amincewa