EFCC Za Ta Daukaka Ƙara Kan Hukuncin Kotun Da Ya ce Ta Biya Emefiele Miliyan 100

Hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ta’annati ta yi watsi da hukuncin tarar naira miliyan 100 da kotun babban birnin tarayya Abuja ta yiwa hukumar kan yadda aka keta yancin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele.

Emefiele ya shigar da karar gwamnatin tarayya, antoni janar da kuma hukumar EFCC domin tabbatar da yancinsa a matsayinsa dan dam.

Ya ce duk da umarnin da kotu ya bayar da a sake shi an cigaba da tsare shi.

A ranar Litinin ne babbar kotun ta bayar da umarnin gwamnatin tarayya da kuma hukumar EFCC su biya Emefiele naira miliyan 100 kan yadda aka keta yancinsa na dan adam.

Da yake mayar da martani cikin wata sanarwa, Dele Oyewale mai magana da yawun EFCC ya ce kotun ta gaza lura da cewa kotu ce ta bayar da umarnin a tsare Emefiele.

Inda ya ce tabbas za su tunkari kotun daukaka kara domin ta jingine hukuncin.

More News

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...