EFCC ta kama Rochas Okorocha

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha, kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

EFCC ta tafi da Rochas daga gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja da yammacin Talata.

Jami’an EFCC da ƴan sanda sun yi dirar mikiya tare da mamaye gidan tsohon gwamnan, inda rahotanni suka ce an yi harbi a ƙoƙarin kama shi.

Hukumar EFCC ta ce matakin ya biyo bayan ƙin amsa gayyatar da tsohon gwamnan ya yi bayan tsallake belin da ya samu a farko.

A ranar 24 ga watan Junairun shekarar 2022 ne EFCC ta shigar da kara a gaban kotu tana tuhumar Okorocha da laifuka 17 da suka hada da karkatar da kudaden al’umma da kadarori da suka kai naira biliyan 2.9.

Hukumar ta ce yunƙurin gurfanar da Sanata Okorocha sau biyu ya ci tura sakamakon ƙin amsa gayyatar da aka yi ma shi.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]