EFCC ta kai samame gidann tsohon gwamnan Zamfara

Abdula'azirz Yari
Image caption

Abdula’azirz Yari ya mulki jihar tsawon shekara takwas daga 2011 zuwa 2019

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC, ta kai wani samame gidan Abdul’aziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ta Najeriya.

Bayanai sun ce kusan jami’ai 20 ne na hukumar suka isa gidan tsohon gwamnan a garin Talata Mafara.

Kakakin hukumar, Tony Orilade ya tabbatar da cewa hukumar ta kai wannan samamen, ya kuma ce sun yi haka ne a dalilin wani bincike da suke gudanarwa.

Ya ce, “Zan iya tabbatar muku cewa jami’anmu sun kai wannan samame zuwa gidan tsohon,” amma bai yi karin haske ba.

Kakakin tsohon gwamnan Ibrahim Dosara ya tabbatar wa BBC aukuwar wannan lamarin a ranar Asabar da daddare, amma ya ce jami’an na EFCC ba su dauki wani abu daga gidan ba.

Rikicin siyasa

Tsohon gwamnan na Zamfara ya dade yana wasan kura da ofishin jam’iyyar APC mai mulki na kasa tun bayan matsalar zaben fitar da gwani a watan Oktobar 2018.

Yari ya zabi wani tsohon kwamishinan kudi da yayi aiki a karkashinsa, wato Mukhtar Idris domin ya gaje shi a matsayin gwamna.

Sannan tsarin da Abdul’aziz Yarin ya so a bi na gudanar da zabukan fitar da gwanin ya raba kawunan ‘yan siyasar jihar ne a karshe.

Ya so jam’iyyar APC ta kasa ta amince da tsarin da zai ba jiga-jigan jam’iyyar ta jiha su zabi wakilan da daga baya za su zabi ‘yan takara, amma uwar jam’iyyar ta ki amincewa da shirin.

A madadin haka, sai ta umarci da a ba dukkan ‘ya’yan jam’iyyar a jihar damar zaben ‘yan takarar da suke so kai tsaye.

Matsalar ta kara tabarbarewa ga tsohon gwamnan bayan da uwar jam’iyyar ta rusa kwamitin zaraswa na jam’iyyar a matakin jiha ana kwana uku da karewar wa’adin gudanar da zabukan fitar da gwani.

Jam’iyyar ta kuma zargi tsohon gwamnan da yin katsalandan cikin ayyukan jam’iyya a jihar.

Wannan ne dai ya sa a karshe bayan bangaren Yari sun yi nasara a babban zanben, Kotun Koli ta soke nasarar sannan ta bai wa jam’iyyar PDP wacce ta zo ta biyu.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...