Dutse mai aman wuta na ci gaba da barna a New Zealand

Dutsen ya fara aman wuta tun ranar Litinin

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dutsen ya fara aman wuta tun ranar Litinin

Yan sanda a New Zealand sun ce har yanzu babu wata alamar cewa mummunan yanayin da ake ciki a tsibirin White Island ya canza a kan haka ba za a iya gudanar da aikin ceto sauran wadanda suka makale a tsibirin ba, bayan fashewar dutse mai aman wuta ranar Litinin.

Sufetan ‘yan sandan Bruce Bird ya fada wa ‘yan jarida cewa suna ci gaba da duba yiwuwar shiga tsibirin da zarar sun samu dama.

Tun farko fira minista Jacinda Arden ta ce tana fatan ganin ‘yan sanda sun samu shiga yankin.

Hakkin mallakar hoto
Google

Ta kara da cewa babban abin da ke gaban masu aikin ceton a yanzu shi ne su ga cewa an ceto rayukan wadanda suka jikkata da ke asibitoci daban-daban da ke fadin New Zealand.

Hakkin mallakar hoto
Michael Schade

Image caption

Munin yanayi ya hana jami’ai shiga cikin tsibirin

To amma ministan rundunar ‘yan sandan New Zealand ya sanar da cewa har yanzu akwai gurbataccen hayaki da ke ci gaba da bazuwa a tsibirin.

Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane shida kuma gwammai sun jikkata, yayin da ake kan neman wasu da dama.

More News

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Aƙalla mayaƙan Boko Haram biyu ne suka miƙa kansu ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a yankin gabashin jihar Borno. Mayaƙan biyu...

Isa Dogonyaro ĆŠan Majalisar Tarayya Daga Jihar Jigawa Ya Rasu

Isa Dogonyaro wakilin al'ummar ƙananan hukumomin Garki da Baɓura a majalisar wakilai ta tarayya ya rasu. Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin a majalisar tarayya,...

Zargin badaƙala: Kotu ta hana Hadi Sirika fita ƙasar waje

A ranar Alhamis ne babbar kotun birnin tarayya Abuja ta hana tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, diyarsa Fatimah da sirikinsa Jalal Hamma...

Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da Ć´arsa

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma wasu mutane uku kan...