Dubban mutane sun fito zanga-zanga a Landan

Protesters outside Parliament

Hakkin mallakar hoto
EPA

Dubban jama’a masu zanga-zanga ne suka taru a tsakiyar Landan, duk da gargaÉ—in da ‘yan sanda suka yi na hana zanga-zanga.

Rahotanni sun bayyana cewa an jefi ‘yan sanda da kwalabe a wani wuri da ake kira Parliament Square, inda wasu rukunin jama’a ke cewa suna kare gumakan garin ne daga masu zanga-zanga kan nuna wariyar launin fata.

‘Yan sanda a Landan din sun haramta wa Æ™ungiyoyi daban-daban zanga-zanga, biyo bayan rikice-rikicen da aka samu a makon da ya gabata.

Daga cikin zanga-zangar, akwai masu iƙirarin muhimmancin baƙar fata, wato Black Lives Matter, inda aka yi irin wannan zanga-zanga a wurare daban-daban ciki kuwa har da tsakiyar Landan.

WaÉ—anda suka haÉ—a zanga-zangar kare gumakan sun buÆ™aci jama’a da kada su haÉ—a hannu da masu zanga-zangar Æ™in jinin wariyar launin fata sakamakon za a iya samun arangama da masu ra’ayin riÆ™au.

Sai dai wasu masu zanga-zangar sun taru a wurin tunawa da waÉ—anda suka yi yaÆ™in duniya na farko wato ‘Cenotaph war memorial,’ da kuma wurin da aka gina gunkin Winston Churcill a Parliament Square a ranar Asabar.

Ƙungiyoyi da dama daga faÉ—in Æ™asar, ciki har da masu tsatsauran ra’ayi suka ce sun shigo Landan ne domin su kare tarihi.

An kewaye gunkin Winston Churcill domin kare shi daga lalatawa, tun bayan da masu zanga-zangar suka fara kirari da cewa ya kasance mai nuna wariyar launin fata lokacin da yake a raye.

Masu zanga-zangar sun rera taken Ingila inda kuma suke kiran “Ingila,” duk da cewa wurin ya É—auki É—umi ganin cewa ga ‘yan sanda a kewaye.

Hakkin mallakar hoto
EPA

  • George Floyd: Tarihin gumakan da masu zanga-zanga suka karairaya

ÆŠaya daga cikin rukunin masu zanga-zangar sun isa inda fadar Firaiminista take wato Downing Street inda suka yi wa wurin Æ™awanya, amma duk da haka sai da aka rinÆ™a jifar ‘yan sanda.

Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel ta wallafa É—aya daga cikin bidiyon arangamar da aka samu yayin zanga-zangar inda ta ce wannan “zanga-zangar ta saÉ“a wa doka”.

“Duk wanda ya tayar da rikici ko kuma ya lalata dukiya, zai fuskanci fushin hukuma,” kamar yadda ta wallafa.

“Ba za mu yarda da kai wa ‘yan sandanmu hari ba.”

Ta Æ™ara jaddada cewa cutar korona “barazana ce a garemu,” ta kuma buÆ™aci mutane da su koma gidajensu.

Hakkin mallakar hoto
EPA

‘Yan sandan sun bayyana cewa sun ayyana doka mai laba 60 har sai karfe 02:00 agogon BST ranar Lahadi, inda dokar ta bayar da dama ga jami’an tsaro da su tsayar da mutane tare da yin bincike ko kuma caje su.

Cikin matakan da aka ɗauka, an buƙaci a daina zanga-zangar zuwa karfe 17:00 agogon BST a ranar Asabar.

‘Yan sandan sun bayyana cewa sun É—auki wannan mataki ne sakamakon sun samu labarin wasu za su shiga garin Landan domin su tayar da zaune tsaye.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...