Diabetes burnout: ‘Ciwon suga ya jawo min matsalar ƙwaƙwalwa’

  • Daga Claire Kendall da Jeremy Cooke
  • BBC News
Bayanan hoto,
Naomi ta yi ta fama da cutar sugar nau’in type 1 da aka gano tana ɗauke da ita

“Aiki ne da babu ranar barin sa. Wani babban nauyi ne da ba ka nema ba sannan ba ka tsammata ba.”

Naomi mai shekara 33 ta gano tana ɗauke da ciwon suga na matakin farko wato type 1 a lokacin da take da shekara 19, ta kuma ce sai da ta kai matakin da ba za ta iya jurar matsalolin lafiyar jiki da na ƙwaƙwalwa da ciwon suga ke jawowa ba, wani yanayi da ake kiran sa “diabetes burnout”.

Kusan mutum 250,000 a Ingila suna da ciwon suga type 1, abin da ke nufin jiki ba zai iya samar da sinadarin insulin ba, sinadarin da ke daidaita yanayin sikarin da ke jikin mutum.

Zai ya jawo lalacewar ɓangarorin jiki da matsalolin ido – a wasu lokutan idan ya yi tsanani ma – har sai an yanke wa mutum wani ɓangare na jikinsa.

Amma ga wasu da dama akwai kuma muhimmin tasirin da yake musu na koyon yadda za su iya shawo kan lalaurar.

Naomi na jin cewa ba za ta iya jure ci gaba da gwada yanayin sikarin da ke cikin jininta ba sau da dama a kowace rana don auna yawan sinadarin insulin ɗin da take buƙatar yin allurarsa, duk da cewa ta san yin hakan wasaere ne da yanayin lafiyarta tare da sa kanta a mummunan hatsari, na shiga matakin ciwon suga mafi tsauri da ake kira diabetic ketoacidosis (DKA), wanda zai iya kai ta ga doguwar suma ta tsawon lokaci.

Sannan ta kamu da rashin lafiya mai tsanani har aka kwantar da ita a asibiti a sashen kula da waɗanda tsarin cin abincinsu ya taɓarɓare, duk da cewa ba ta samun matsala wajen cin abinci.

Shugaban sashen, Dr Carla Figueirdo, ta yi magana kan marasa lafiyarta masu ciwon suga: “Waɗannan mutane ba su da lafiya sosai, ba su da lafiya sosai.

“Suna sa kansu a cikin hatsari a kowace rana idan har ba su yi allurar insulin ɗinsu ba.

Babbar likitar da ke duba Naomi a Asibitin Royal Bournemouth, Dr Helen Partridge, ta ce bai kamata a ƙi ɗaukar batun lafiyar ƙwaƙwalwar da ke da alaƙa da cwion suga da mihimmanci ba.

Bayanan hoto,
Dr Partridge ta ce rayuwa da matsalar ƙwaƙwalwa ga masu cutar suga babban al’amari ne

Ta ce “Dole ku koyi rayuwa da wannan cuta a kullum rana ta Allaj.”

“Abin taƙaicin shi ne ba za a taɓa warkewa gaba ɗaya ba.

“Sannan kuma tasirinta a kan lafiyar ƙwaƙwalwa na da girma sosai.”

Ƙoƙarin inganta abubuwa

Asibitin na lura da ɗaya daga cikin wani aikin gwaji na Hukumar Lafiya Ta Ingila NHS yadda za a yi wa masu lalurar nau’in type 1 na cutar suga magani, waɗanda tsananin cutar ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

Likitan da ke jagorantar shirin na NHS Farfesa Partha Kar ya ce: “Shirin na NHS mai dogon zango ya mayar da hankali ne kwacakom kan yadda za a shawo kan cutar suga da matsalar ƙwaƙwalwa a lokaci guda.

“Idan har muka magance waɗannan abubuwa biyu a lokaci guda, to za a samu sakamako mai ma’ana.”

Naomi, wacce a yanzu ta bar sashen, ta ce: “Na yi matuƙar jin daɗi da yabawa zuwana nan, duk da irin tsoron da ya ba ni.

“Kuma na gode wa tawagar da take nan sosai.”

Aikin gwajin ya taimaka wa fiye da mutum 70 da suka haɗa da Naomi, waɗanda da yawansu, tawagar ta ce, da haka za su ci gaba da rayuwa ba tare da an gano abin da ke damunsu ba.

Kuma ko ita ma Naomi a yanzi tana jin cewa rayuwarta ta gaba za ta inganta.

“Kuma ko da babu waraka gaba ɗaya, akwai kyakkyawan fata,” a cewarta, “Ko yaushe akwai fata. Kuma a kullum mun fi so mu rayu.

“Don haka wannan dama ce ta zaɓar rayuwa.”

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...