Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja.
Gawarwakin sun iso ne da misalin ƙarfe 2:39 na rana a cikin motocin daukar marasa lafiya daban-daban.
Rahotanni sun nuna cewa wasu fusatattun matasa ne a yankin Okuama suka kashe jami’an soji da suka haɗa da manyan sojoji hudu, da kananan sojoji 13 a ranar 14 ga watan Maris.