Dattawan Arewa sun nemi Fulani makiyaya su dawo Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi Kira ga Fulani Makiyaya da ke kudancin kasar da su koma Arewa.

A daidai lokacin da jam’iyyar adawa ta PDP ke kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a bangaren tsaro, Kungiyar Dattawan Arewa karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ta yi kira ga dukanin makiyaya da ke kudancin kasar, da su tattara nasu ‘inasu su koma Arewa.

Abdullahi ya yi wannan kira ne inda ya yi ikrarin cewan ba za a ba su kariya ba saboda ka’idar da gwamnonin shiyyar kudancin kasar suka samar wa makiyaya, da ke cewa sai dai su rika diban dabbobinsu a mota amma ba dai su yi kiwo a kasa ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi binciken abubuwan da ke faruwa saboda a yi wa kowa adalci idan za a biya diyya bayan sun dawo gida.

Sai dai daya daga cikin shugabannin Gammaiyar Kungiyoyin Matasan Arewa Sherrie Nastura Ashir, ya ce an sha yin irin wadannan tarurukan tun a zamani Marigayi Abacha, amma kuma duk ba su yi wa kasa amfani ba.

Yanzu kiran da suke yi shi ne, a kafa Kwamitin raba gardama, saboda duk wanda yake so ya zauna a Najeriya a ba shi dama ya zauna a duk inda yake so.

A lokacin hada wannana rahoton dai fadar shugaban kasa ba ta ce komai akan wannan lamari ba.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...