Darajar naira ta yi kasa a yayin da ake canza dala a kan N1045

Darajar Naira tayi faduwar da bata taba yi ba a kasuwar bayan fage a ranar Laraba.

Wasu masu wurin hada-hadar canjin kudade sun bayyana cewa suna sayar da kowace dalar Amurka kan N1045.

Hakan na nufin darajar ta Naira ta yi kasa da naira 45 idan aka kwatanta da farashinta cikin makonni biyu.

Yan canjin kuÉ—in sun bayyana cewa suna sayan dalar Amurka akan 1020 su kuma sayar 1045.

“A yanzu haka dalar Amurka na karanci” a cewar Aliyu wani mai canjin kuÉ—i a birnin Lagos.

A kasuwar musayar kudade ta bankuna ana sayar da kowace dalar Amurka kan kuÉ—i naira N776.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...