Dalilin Da Ya Sa Na Daina Yawon Sulhu Da ‘Yan Bindiga – AREWA News


Watanni biyu da suka gabata, Sheikh Ahmad Gumi ya shiga wani rangadi a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ya ke ziyartar shugabanni da kuma ‘yan bindiga da ke cikin daji, tare da zimmar jagorantar tafarkin sasantawa tsakanin ‘yan bindigar da gwamnati.
Daga bisani kuma malamin ya dakatar da wannan rangadin ba tare da wani bayani ba na tsawon lokaci.
To amma a yanzu Gumi ya ce ya dakatar da yunkurin na neman sulhu da ‘yan bindigar ne, saboda gwamnatin jihar Kaduna da ma ta tarayya ba sa ra’ayin sulhu da ‘yan bindigar.
A cikin wata sanarwa da jami’insa na watsa labarai Salisu Hassan ya fitar, Sheikh Gumi ya ce ya janye daga kokarin sasantawar ne domin mutunta matsayar gwamnati akan lamarin.

Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga
Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga

“Ba wai ayuka ne suka yi wa Sheikh yawa ba. Matsalar ita ce gwamnati ba ta da sha’awar sulhuntawa ta wadannan mutanen. Saboda haka Sheikh ya yi kokarin bin wasu hanyoyi domin cimma burinsa,” in ji Salisu Hassan.
Ko baya ga ziyartar shugabanni, Sheikh Gumi ya yi tattaki zuwa wasu dazuka a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Naija, inda ya sadu da ‘yan bindigar da suka addabi yankin da hare-hare, kisan jama’a da satar mutane domin karbar kudin fansa.
Malamin yayi wa ‘yan bindigar wa’azi, tare da shawartar su da su ajiye makamai, su shigo gari domin gwamnati ta yi musu afuwa, su kuma su daina miyagun ayukan da suke yi.

Sheikh Ahmad Gumi ya ziyarci 'yan bindiga a dajin jihar Zamfara
Sheikh Ahmad Gumi ya ziyarci ‘yan bindiga a dajin jihar Zamfara

To sai dai tuni matakin na Gumi ya hadu da kakkausan suka daga wasu shugabanni kamar gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ma shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Haka kuma jawaban malamin akan abin da ya bayyana a matsayin “danne hakki da ‘yancin mutanen ne ya sa su daukar makamai suka shiga daji,” sun ja hankalin manazarta lamurran tsaro, masu ganin cewa kalaman malamin na da hatsarin gaske ga sha’anin tsaron kasa.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufa’i na daga cikin shugabanni na farko da ya soma yin fatali da shawarar Gumi, inda ya sha alwashin cewa sam bai ga dalilin yin sulhu da ‘yan ta’adda ba.
Saurari kalaman Gwamna El-Rufa’i dangane da zancen yin sulhu da ‘yan bindiga.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa bayan ziyarar dazukan, Sheikh Gumi ya yi kokarin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin tattaunawa akan abin da ya gano daga ziyarar ta shi, da kuma yiwuwar shata tafarkin yin sulhu da afuwa ga ‘yan bindigar da ke da bukatar ajiye makamai.
To sai dai rahotannin sun ce bayan kwashe tsawon fiye da wata daya yana yunkurin, malamin bai sami nasarar ganin shugaban kasar ba, lamarin da kuma ya sanyaya masa gwiwar ci gaba da kokarin samar da sulhu da afuwa ga ‘yan bindigar.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...