Da ya harbi mahaifinsa a wajen farauta | BBC Hausa

A boar in Sardinia

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matashin ya harbi mahaifin nasa ne a yayin farautar aladen daji

‘Yan sandan kasar Italia sun tuhumi wani mutum da laifin kisa da gangan bayan da ya harbi mahaifinsa wanda kuma ya ce ga garinku nan sakamakon farautar aladen daji.

Kafafen watsa labaran kasar ta Italiya dai sun ce al’amarin ya faru ne lokacin da mutanen biyu ke kutsawa cikin dokar dajin da ke kusa da garin Postiglione a lardin kudancin Salermo, ranar Lahadi.

Matashin mai shekara 34 ya bude wuta lokacin da ya ga giftawar inuwa da motsin ganyaye, inda ya durka wa mahaifinsa dalma a ciki.

Faruwar hakan da wuya sai matashin ya kwarmata ihun neman dauki bayan fahimtar cewa mahaifinsa ya harba ba dabba ba.

  • An kama ‘barayin’ jarirai a Legas
  • Marasa karfi su rage yawan aure-aure — Sarkin Zamfarar Anka

To sai dai likitoci ba su iya cetar ran Martino Gaudioso mai shekara 55 ba.

An dai ce dan da mahaifinsa na yin farauta ne a gandun dajin da aka haramta yin farautar dabbobi a cikinsa ne. Tuni kuma ‘yan sanda suka kwace bindigogin mutanen biyu.

A ranar Lahadi ne dai shugaban kungiyar masu rajin kare hakkokin dabbobi da muhalli ya ce Italiya ta zama ‘abin tsoro’.

A watan Oktoban da ya gabata ne ministan muhalli na kasar, Sergio Costa, ya yi kira da ga kasar da ta haramta yin farauta ranar Lahadi, bayan da wani matashi dan shekara 18 ya mutu sakamakon harbe shi da aka yi a kan iyakar kasar da Faransa.

A karshen watan Oktoban dai an samu rasa ran mutum biyu a irin wancan yanayi.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...