Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a Cibiyar Kula Da Lafiya ta Tarayya dake Jalingo sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa.
Mai riƙon muƙamin shugaban sashen asibtin kwantar da marasa lafiya na cibiyar, Joseph Kuni ya ce an samu mace-macen ne a tsakanin watan Janairu- Faburairun shekarar 2024.
Ya ce akwai marasa lafiya 10 dake sashen da ake killace masu ɗauke da cutuka masu yaɗuwa inda suke jiran sakamakon gwajin da aka yi musu.
“Mun tura samfurin jini 105 an samu 60 daga ciki na da cutar Lassa a yayin da babu cutar a 39 muna kuma cigaba da sauraron sauran,” ya ce.
Kwamishinan lafiya na jihar,Gbangsheya Buma ya tabbatar da ɓarkewar cutar a jihar.
Buma ya ce mutane 8 cikin waɗanda aka yiwa gwajin cutar a ranar Juma’ar da ta gabata suna ɗauke da cutar.