Cutar Zazzaɓin Lassa Ta Kashe Mutane 19 A Jihar Taraba

Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a Cibiyar Kula Da Lafiya ta Tarayya dake Jalingo sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa.

Mai riƙon muƙamin shugaban sashen asibtin kwantar da marasa lafiya na cibiyar, Joseph Kuni ya ce an samu mace-macen ne a tsakanin watan Janairu- Faburairun shekarar 2024.

Ya ce akwai marasa lafiya 10 dake sashen da ake killace masu É—auke da cutuka masu yaÉ—uwa inda suke jiran sakamakon gwajin da aka yi musu.

“Mun tura samfurin jini 105 an samu 60 daga ciki na da cutar Lassa a yayin da babu cutar a 39 muna kuma cigaba da sauraron sauran,” ya ce.

Kwamishinan lafiya na jihar,Gbangsheya Buma ya tabbatar da É“arkewar cutar a jihar.

Buma ya ce mutane 8 cikin waÉ—anda aka yiwa gwajin cutar a ranar Juma’ar da ta gabata suna É—auke da cutar.

More News

Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar É—aliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar Æ™yanda. A wata sanarwa ranar Litinin,...

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen ÆŠan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen É—an fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...