Cutar Ebola ta fara bazuwa makwabta

wasu ma'aikatan lafiya a asibitin Ebola

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kusan mutane 1,400 cutar Ebola ta kashe kwanan nan a Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo

Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar cewa annobar cutar Ebola wadda ta barke a Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo, ta bazu zuwa makwabciyar kasar, Uganda.

Ma’aikatar lafiya ta Uganda da Hukumar Lafiya ta Duniya sun ce, a yanzu haka ana yi wa wani yaro dan shekara biyar wanda ya fito daga Kongon ya tsallaka zuwa Uganda wanda kuma yake dauke da cutar, magani.

Yaron ya shiga Uganda ne tare da sauran ‘yan uwansa , ranar 9 ga watan nan na Yuni, kuma a yanzu ana masa magani a wani asibiti da ke bangaren Uganda ta iyakar kasashen biyu.

  • Bincike: Masu cutar Ebola na samin tabin hankali
  • Gwamnati ta tuhumi Sheikh El-Zakzaky da laifin kisan kai

Daman dai wannan bazuwa ta cutar Ebola daga Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo zuwa wata kasa makwabciya, abu ne da aka dade ana tsammani, musamman ganin yadda aka jima ana ta gargadi da ankarar da jama’a, sai kuwa ga shi kwatsam ta tabbata.

Tuni dai aka tura masu bayar da agajin gaggawa kan cutar, zuwa wannan yanki domin gano ko akwai wani da shi ma ya kamu da ita ko yake cikin hadarin kamuwa da cutar.

Daman tuni hukumomin Ugandar da hadin guiwar kungiyar agaji ta Save the Children sun ce sun riga sun ba wa ma’aikatan lafiya da masu aikin sa-kai hadi da malaman makaranta sama da dubu hudu horo da riga-kafin cutar, da kuma ba su kayayyakin aiki na maganinta ko da ta ka iya kunno kai kasar.

A shekarar da ta wuce ne annobar cutar mai saurin kisa ta barke sosai a Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo, kuma zuwa yanzu ta hallaka sama da mutane 1400, bayan wasu sama da 2000 da ta kama.

A yau Laraba ne za a yi wani zama na tattaunawa tsakanin jami’an Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongon da Uganda, domin yanke shawarar ko za a kai ‘yan uwan yaron wadanda suke Uganda zuwa wata cibiya ta musamman kan cutar a Kongon domin sanya ido a kansu.

Cutar Ebola dai tana haddasa zubar da jini a cikin mutum da zazzabi mai karfi da kuma amai.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...