Coronavirus ta sauya yadda Musulmi ke ibada

Musulmai ke nan
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
—BBC Hausa, London
Image caption

Wasu kasashe sun hana sallar Juma’a saboda kaucewa yada kwayar cutar Coronavirus

Cutar Covid-19 wadda aka fi sani da Coronavirus ta tilasta wasu daga cikin manyan addinan duniya sauya yadda suke gabatar da ibadunsu a sassa daban-daban.

Musulmi da Kiristoci a kasashen duniya kamar Saudiyya da Iran da Birtaniya da Falasdin da Pakistan da Tajikistan da Singapore da Ghana duk sun samu gargadin kaurace wa wuraren ibada saboda dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Kasashen duniya da dama sun shawarci al’ummarsu kan yadda ya kamata su rika mua’amala da juna, kamar gaisuwa da cin abinci da sauransu.

Saudiyya ta hana ‘yan kasarta aikin Umarah

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Saudiyya ta sanar da dakatar da mazauna kasar daga yin aikin Umarah na wucin gadi a kokarin kasar na hana yaduwar Coronavirus.
Umarah dai bangare ne na babbar ibadar da Musulmi ke yi a kasar Saudiyya, wadda za a iya kammalawa a cikin ‘yan sa’o’i, ba kamar aikin Hajji ba da ke daukar kwanaki.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan ya danganta daukar matakin da kaguwar gwamnatin Saudiyyan na goyon bayan kokarin da duniya ke yi, musamman ma manyan hukumomi irin Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, na hana yaduwar cutar.
A watan da ya gabata ne Saudiyya ta haramta wa ‘yan kasar waje zuwa birnin Makkah da Dakin Ka’aba sannan ta hana kai ziyara kabarin Annabi Muhammad SAW.
Ana sa ran yin aikin Hajji na bana a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba game da batun.
Zuwa yanzu mutum biyu ne suka kamu da cutar a Saudiyya.

Za a rufe cocin garin Bethlehem a Falasdinu

Hakkin mallakar hoto
AFP

Za a rufe cocin Nativity da ke garin Bethlehem – garin da Kiristoci suka yi amannar an haifi Yesu Almasihu – a wani bangare na dakile yaduwar cutar.
Hakan ya biyo bayan wasu mutum hudu da ake zargi sun kamu da cutar.
Tuni gwamnatin Falasdinawa ta bayar da umarnin rufe duka coci-coci da masallatai da ma dakunan otal “domin hana baki ‘yan kasar waje shiga garin Bethlehem”.
Garin da ke cikin Falasdin a yankin West Bank wanda kuma Isra’ila ta mamaaye, ya dogara ne kacokam kan ‘yan yawon bude ido don samun kudin shiga.

Iran ta hana sallar Juma’a

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kasar Iran ma tana ta fama da cutar, inda masu dauke da ita ke ci gaba da karuwa.
Ba a gudanar da sallar Juma’a ba a dukkanin manyan garuruwan kasar.
Shugaban kasar Hassan Rouhani ya fada wa majalisar ministocinsa cewa “wannan cuta ta zama ruwan dare”.
Ya kara da cewa: “Ta kama kusan dukkanin sassan kasarmu sannan kuma ta karade duniya baki daya. Dole ne mu yi iyakar bakin kokarinmu da aiki tare domin kawo karshenta.”
Zuwa yammacin ranar Laraba, mutum 2,922 ne suka kamu sannan 92 suka mutu a kasar ta Iran.

An hana watsa ruwa mai tsarki a coci-cocin Katolika a Birtaniya

Cocin Katolika ta yi gargadi game da taron bai wa mabiya ket mai tsarki wato Communion da kuma watsa ruwa mai tsarki a coci-coci saboda tsoron Coronavirus.
Kungiyar Bishops’ Conference of England and Wales (CBEW), mai kula da ayyukan cocin Katolika a Birtaniya, ta bayyana yadda ya kamata a rika yin taruka domin dakile yaduwar cutar.
A watan da ya gabata CBEW ta shawarci ‘yan Katolika da suka ji alamun mura da su kaurace wa karbar ket mai tsarkin a kan harshensu ko kuma daga kofin Chalice.

Tajikistan ta umarci Musulmi su yi sallah a gida

Kasar Tajikistan wadda ba ta samu bullar Coronavirus ba, ta dakatar da sallar Juma’a.
Kasar da ke da yawan mutane miliyan tara wadda kuma Musulmi ke da rinjaye, ta kulle iyakokinta ga makwabtanta – China da Afghanistan – sannan ta hana ‘yan kasashen Koriya ta Kudu da Iran da Italiya shiga kasar.
Kazalika ta haramta bukukuwan murnar sabuwar shekara na Persian New Year, wadanda ake gudanarwa daga 21 ga watan Maris zuwa 25.
Minista a Singapore ya shawarci Musulmi da amfani da daddumarsu, su daina musabaha
Jaridar The Straits Times ta ruwaito Minista mai kula da harkokin addini a kasar Singapore, Masagos Zulkifli yana shawartar Musulmi da su je masallatai da abin sallarsu daga gida sannan kuma su guji yin musabaha da juna.
“A irin wannan yanayi, ba za mu rika musabaha da juna ba, amma idan kun yi to ku wanke hannayenku sannan ku tabbata ba ku taba fuskarku ba,” in ji ministan.
Yayin da tantance yanayin zafin jikin mutane zai yi wuyar gaske a masallatai saboda yawan masallata, Masagos ya ce duk Musulmin da ya ji alamun rashin lafiya ya zauna a gida.
Akwai wadanda suka kamu da Coronavirus fiye da 100 a Singapore, amma mafi yawan wadanda suka kamu sun warke.

Kungiyar Musulmi a Birtaniya ta shawarci Musulmi da su bi umarnin gwamnati

Daya daga manyan kungiyoyin Musulmi a Birtaniya mai suna Muslim Council of Britain (MCB) ta yi kira ga masallatai da cibiyoyin Musulunci da su “tsare tarukansu” ta hanyar bin shawarwarin gwamnati kan Coronavirus.
MCB ta rubuta a shafinta na intanet cewa akasarin wadannan shawarwari sun dace da koyarwar Annabi Muhammad(SAW).
Ta ce: “Abu Malik Al-Ash`ari ya ruwaito cewa Annabi ya ce: ‘Tsafta rabin imani ce.'”
Ta shawarci masallatai da makarantu da su karfafa wa jama’a gwiwar yawan wanke hannu sannan kuma su tanaadi isasshen sabulu musamman a kusa da wuraren alwala.
Mutanen da suka kamu da cutar a Birtaniya sun kai 116.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...