Coronavirus: Sadio Mane ya bai wa Senegal tallafin £41,000

Mane

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mane ya yi kira a dauki batun yaduwar cutar ta coronavirus da “matukar muhimmanci.”

Dan wasan Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane ya bayar da gudunmawar £41,000 ga kwamitin da kasarsa ta nada domin yaki da cutar coronavirus.

Dan wasan ya dauki matakin ne bayan da ya lura da yadda cutar ke yaduwa a kasar ta Senegal.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mane ya yi kira a dauki batun yaduwar cutar ta coronavirus da “matukar muhimmanci.”

Dan wasan ya bai wa magoya bayansa shawara kan matakan da za su dauka domi kare kansu daga kamuwa da cutar, kamar “wanke hannu tsawon dakika 30”.

Kawo yanzu, an tabbatar da mutum 27 da suka kamu da Covid-19 a Senegal, ko da yake biyu dsaga cikin su sun warke, a cewar ma’aikatar lafiyar kasar.

Hukumomina Senegal sun sanar da dakatar da sauka da tashin jiragen sama tsakanin kasashen yammaci da arewacin Afrika, da kuma wasu kasashen Turai da dama. (Faransa da Spaniya da Italiya da Belgium da kuma Portugal)

A arewacin Afrika kuwa kasashe kamar Aljeriya da Tuniya yayin da Morocco tuni ta dakatar da saukar jirage daga Senegal din.

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...