Coronavirus: Fiye da Amurkawa 250,000 suka mutu saboda cutar korona

A patient taken into a hospital in Brooklyn

Wadanda suka kamu da cutar korona a Amurka sun zarce mutum 250,000, wanda ke nuna gagarumar gazawa a fagen yaki da annobar da ke sake yaduwa a fadin kasar.

Kamar yadda wani rahoto da Jami’ar Johns Hopkins ta fitar, kasar na da adadin mutum 250,029 da su ka rasa rayukansu, inda mutum miliyan 11.5 kuma suka kamu.

Ita ce kasar da ke kan gab wajen yawan masu fama da cutar da ma adadin wadanda suka mutu tsakanin dukkan kasashen duniya.

Yayin wata hira da yayi da BBC, babban jami’i mai kula da sashen yaki da cututtuka masu yaduwa na Amurka, Dokta Anthony Fauci ya ce kasar “ta kaucewa hanyar da ya dace ta bi a wannan lokaci maii matukar hatsari,” wanda zai tilasta wa mutane kunshewa cikin gida saboda isowar hunturu.

Wannan labarin na zuwa ne a daidai lokacin da birnin New York – wanda shi ne cibiyar masu fama da cutar korona a ‘yan watannin baya – ya kulle dukkan makarantu daga ranar Alhamis saboda kara yaduwar da cutar ke yi.

Shawarar rufe makarantun ya zama tilas ne saboda yawan masu kamuwa da cutar ya zarce kashi daya cikin 100 na al’ummar jihar. Ana sa ran yara 300,000 za su kamu da cutar.

Bayanan hoto,
Wasu dalibai a New York sun rika daukan darussa a filin Allah ne a watan Satumba

A wata hira da yayi da BBC, Dakta Fauci ya gargadi Amurkawa da su mayar da hankali kan yadda cutar ke kara yaduwa, wanda ka iya kashe mutane masu dimbin yawa

“Wannan yanayi ne mai hatsari sosai saboda akwai alamun da ke nuna haka,” inji shi.

Ya kuma ce “idan aka sami gagarumin kari a adadin masu kamuwa da cutar, kamr yadda muke gani a yanzu, kasancewar mutane sun fi zama a cikin gidajensu zai dagula lamurra.”

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuÉ—aÉ—e

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...