Coronavirus: Fafaroma zai daina ibada a bainar jama’a

Hakkin mallakar hoto
Reuters

—BBC Hausa

Fafaroma Francis na darikar Katolika zai gabatar da jawabinsa na ranar Lahadin yau ta hanyar amfani da bidiyo maimakon kai tsaye kamar yadda ya saba yi ga dubban mabiya darikar Katolika.

A kan gudanar da wannan taron ibada ne a dandalin Saint Peter da ke cikin Vatican.

Wannan matakin ya taso ne ne saboda fargabar kamuwa da cutar Coronavirus.

Daga yanzu Fafaroman zai rika nadar jawabinsa ne yana turawa ta intanet har zuwa lokacin da aka shawo kan cutar. A makon jiya ne dai aka gano mutum na farko da ya ake dauke da kwayar cutar ta Covid-19 a Fadar ta Vatican.

Shekara 66 ke nan a tarihi da jerin Fafaroma ke gabatar da addu’o’i ga mabiya darikar Katolika daga sassa daban daban na duniya, inda karon farko ke nan da aka sami wani Fafaroma ya kauracewa wannan al’ada.

Jami’ai a fadar Vatican sun ce saboda rage yawan cunkoso da ka iya ba cutar coronavirus damar ci gaba da yaduwa, daga ranar Lahadi, Fafaroma Francis ba zai ci gaba da bayyana a dandalin Saint Peter ba.

A madadin haka zai rika aika wa da sakon bidiyo ne kai tsaye daga cikin Fadar Apostolic.

Kuma ranar Laraba mai zuwa – ranar da ya saba ganawa da mabiya darikar a kowane mako – Fafaroman ba zai fita wajen fadar ba.

Fadar Vatican, wadda ita ce kasa mafi kankanta a duniya ta bayyana bullar cutar ne a makon jiya.

Kuma Fafaroman mai shekara 83 da haihuwa na fama da matsananciyar mura na fiye da mako guda, ko da yake jami’ai a Vatican din sun ce murar ba ta da alaka da nau’in cutar Covid-19.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A daya bangaren kuma, cutar sai kara bazuwa ta ke yi a fadin kasar Italiya, wanda zuwa ranar Asabar an bayyana cewa mutum fiye da 1,200 ne suka kamu da cutar.

Kawo yanzu dai adadin masu cutar sun kai 6,000 kuma an tabbatar da mutuwar mutum fiye da 230 a kasar ta Italiya.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...