Coronavirus a Afrika: Janyewar Amurka daga WHO barazana ce ga Afirka

Trump

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A karshen watan Mayu Trump ya ce: “Za mu katse alakarmu da WHO kuma za mu karkatar da kudaden da muke bata a wasu fanonin da suke bukatar tallafi”

A farkon wannan makon shugaban Amurka Donald Trump a hukumance ya fara shirye-shiryen fitar da ƙasarsa daga hukumar lafiya ta WHO.

A watan Mayun da ya gabata shugaban ya bayyana karara cewa Amurka ba za ta ci gaba da zama a hukumar ba, bayan ya zargi cewa China ke juya akalarta, yayin da ake tsaka da barkewar annobar korona.

Duk da cewa kasashe da dama har da Turai sun roki Trump kan ficewa daga WHO, shugaban ya ce zai balle daga hukumar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya sannan ya karkatar da kudaden da Amurka ke bayarwa zuwa wani fannin.

A halin yanzu dai ya tura wa Majalisar Dinkin Duniya da Majalisar Amurka aniyarsa, ko da yake matakin ficewar zai kai shi a kalla shekara guda.

Matakin zai shafi yaki da Corona?

A tattaunawar BBC da Dokta Nasir Sani Gwarzo, kwararre kan cutuka masu yaduwa, ya ce janyewar Amurka zai kawo cikas matuka domin bayan gudunmawar ma’aikata da kimiya da bincike akwai zunzurutun kudaden da take bai wa WHO.

“Wannan zai shafi yakin da ake da annobar cutar korona domin har yanzu ba a kawo karshenta ba, janyewar Amurka zai haddasa gibi a kokarin samar da riga-kafi.

“Yadda cutar take a yanzu abu ne mai wahala a iya kawo karshenta a yanzu ga kuma takaddama, don haka ci gaba da bincike da ba da shugabanci ga kasashe na yaki da wannan cuta zai fuskanci tasgaro.”

Dokta gwarzo ya ce yanayin da cutar ke nunawa a yanzu da wuya ta kare nan kusa, domin ta dauko matakan karuwa a duniya, ana iya kai shekara daya ko biyu a wannan yanayi.

Makomar Afirka

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kasar Amurka ita ce ke ba da kaso mafi tsoka na tallafi ga hukumar WHO, a shekara ta 2019 ta zuba kudaden da yawansu suka haura dala miliyan 400, kusan kashi 15 cikin 100 na kasafin WHO, in ji Dokta Gwarzo

“Amurka ta ce za ta janye idan WHO ba ta gurfanar da China ba da kuma bin wasu ka’idoji da ta gindaya, duk wata kasa da ke dogaro da WHO musamman kan annoba za su wahala.

“Kasashen Afirka kusan su ne sahun gaba wajen samun tallafi idan an samu barkewar annoba don haka za su shiga tsaka mai wuya, hakan zai yi wa Afrika barnar gaske, musamman matalauta kasashe.”

Dokta Gwarzo ya ce idan ba a sasanta ba kuma ba a fito da tsarin habaka WHO ba to ayyukan kungiyar baki daya zai sauya ko ya ma durkushe.

“Duk ranar da kasar da ita ce ta yi fice aka dogara da ita ta yi irin wanan barazana to dole a wahala.

“Akwai bukatar farfado da hanyoyi dogara da kai muddin WHO ta shirya ganin ta tsira musamman daga irin wadanan barazana”.

Me Trump ke cewa?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Afrilu Trump ya soma sanar da cewa Amurka za ta janye kanta a matsayin mambar wannan hukuma -WHO

A watan Afrilu ya soma sanar da cewa Amurka za ta janye kanta a matsayin mambar wannan hukuma -WHO- muddin ba ta sauya tsarin ayyukanta ba a cikin kwanaki 30.

Sannan a karshen watan Mayu ya ce: “Za mu katse alakarmu da WHO kuma za mu karkatar da kudaden da muke bata a wasu fanonin da suke bukatar tallafi”.

“Duniya ta shiga tsaka mai wuya saboda sakancin gwamnatin China,” a cewar Trump, sannan ya zargi China cewa da gangan ta assasa annobar a duniya”.

Shugaba Trump ya zargi China da matsa wa WHO lamba ta hanyar “boyewa duniya gaskiya” a kan cutar, ba tare da shaidu da ke tabbatar da zarge-zargensa ba.

“China ke juya akalar WHO kashi 100 bisa 100,” a cewar Trump.

Sauran kasashen dai irin su Jamus da Burtaniya sun ce ba su da niyya ko tunanin janyewa daga WHO, da ke kokarin hada-kan duniya wajen samar da rigakafin Covid-19.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

WHO da kudaden tallafinta?

  • An kafa WHO a 1948 a Geneva, wani bangare ne na MDD da ke kula da fanin lafiya a duniya
  • WHO na da mambobi 194, makusudinta shi ne “tallafawa fanin lafiya, tabbatar da ingancin lafiya a duniya da taimakawa mabukata”
  • Tana ayukan wayar da kai kan riga-kafi,bukatun gaggawa a fanin lafiya da taimakawa kasashe da ke mataki na farko a lafiya
  • Tana samun tallafi daga kasashe mambobinta’ kudaden da suke bayarwa ya danganci karfin kasa da yawan al’ummarsu da kuma yadda ta kayade zata taimaka.

Karin bayani

Karkashin tsarin dokoki da majalisa ta amince a shekara ta 1948, Amurka na iya janyewa daga WHO amma sai ta ba da sanarwa ta a kalla shekara guda sannan ta biya kudaden da ake bin ta, ko da yake akwai sarkakiya kan matsayar da Mista Trump yake a yanzu.

Janyewar a yanzu zai diga ayar tambaya kan kudaden shigar WHO da kuma makomar shirye-shiryenta na karfafa fanin lafiya da dakile cutuka.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...