Cikin Hotuna: Ziyarar Emmanuel Macron a Nijar

Ranar Lahadi ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyara kasar Nijar domin yin ta’ziyyar sojojin nan 71 da ‘yan bindiga suka kashe.

Image caption

Shugaba Muhamadou Issoufou na Nijar da twkwaransa na kasar Faransa Emanuel Macron sun kai ziyara makabartar da aka binne sojojin Nijar da ‘yan bindiga suka kashe

Image caption

Macron ya kai ziyarar ne a kan hanyarsa ta zuwa kasar Ivory Coast domin yin bikin Kirsimati tare da sojojin kasarsa

Image caption

Kasar Faransa ce tsohuwar uwar gijiyar Nijar, wadda ta yi wa mulkin mallaka shekara 61 da suka gabata

Image caption

Akwai daruruwan dakarun kasar Faransa a kasar ta Nijar, wadanda suke horarwa tare da taimaka wa wasu rundunonin sojan Nijar din

Image caption

Sai dai ziyarar tasa ta gamu da cecekucen daga wasu ‘yan Nijar, inda suka ce ba sa maraba da shi sannan suka zargi Faransa da mara wa ‘yan bindigar baya

Image caption

Wasu ‘yan kasar ta Nijar, har wa yau, sun yi kiran da Faransa ta tattara komatsanta ta bar masu kasarasu

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...