Champions League: Gasa ta 66 za a fara a kakar 2020-21 kuma ta 29 tun sauya fasali

Kakar Gasar Champions League ta 2020-21 ita ce ta 66 da zakarun kungiyoyin nahiyar Turai kan kara a tsakaninsu da hukumar kwallon kafa ta Turai kan shirya.

Kuma ita ce ta 29 tun bayan da aka sauya mata fasali daga European Champion Clubs Cup zuwa UEFA Champions League.

Za a buga wasan karshe a gasar kakar bana a Atatürk Olympic Stadium a Istanbul da ke Turkiya.

Tun farko wannan filin aka tsara zai karɓi baƙuncin karawar karshe a 2020, amma bullar cutar korona ta sa aka dage wasan daga wurin.

Duk wacce ta lashe kofin bana za ta samu tikitin shiga wasannin rukuni kai tsaye a badi a gasar 2021-22, za kuma ta fafata a Uefa Super Cup da wacce za ta lashe Europa League a bana.

Bayern Munich ce ta lashe kofin 2019-20.

Wasannin da za a kara ranar Talata 21 ga watan Oktoba

Group E: Rennes da Krasnodar

Group E: Chelsea da Sevilla

Group F: Zenit da Club Brugge

Group F: Lazio da Dortmund

Group G: Dynamo Kyiv da Juventus

Group G: Barcelona da Ferencváros

Group H: Paris da Man United

Group H: Leipzig da BaÅŸakÅŸehir

Wasu abubuwan da za su ja hankali:

Ko yaya Andrea Pirlo zai fuskanci tsohon kocinsa?

A shekarar 1995 koci, Mircea Lucescu ya fara sa Andrea Pirlo a Gasar ‘Seria A’ dan kwallon yana da shekara 16 a lokacin.

Shekara 25 tsakanin Lucescu shi ne kocin Dynamo Kyiv a yanzu da zai fuskanci Pirlo wanda a karon farko zai ja ragamar Juventus a gasar Champions League.

Shin ko Pirlo mai shekara 41 zai doke tsohon kocinsa a karawar da Cristiano Ronaldo ba zai buga ba, sakamakon killace kansa, bayan da ya kamu da cutar korona?

Ko Messi zai rage tazarar ƙwallaye da ke tsakaninsa da Ronaldo a wasan Ferencváros?

Cristiano Ronaldo ya killace kansa, bayan da ya kamu da cutar korona a lokacin da ya je buga wa tawagar Portugal tamaula.

Wannan dama ce da Lionel Messi zai rage tazarar kwallo 15 da ke tsakaninsa da dan wasan Juventus a matakin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Gasar ta Zakarun Turai ta UEFA Champions League.

Ko Immobile zai nuna wa Dortmund bajintarsa?

Dan wasan Lazio, Ciro Immobile ne ya lashe takalmin zinare a nahiyar Turai a matakin wanda ke kan gaba a yawan cin ƙwallaye a raga a kakar bara.

Immobile shi ne ya maye gurbin Lewandowski a Dortmund, bayan da daban kwallon ya koma Bayern in 2014, sai ya kasa taka rawar gani inda da kyar ya ci kwallo 10 a wasa 34 da ya yi.

Da yake Lazio za ta karbi bakuncin Dortmund ranar Talata, wannan dama ce da dan wasan mai shekara 30 zai nuna shi ba kanwar lasa bane.

Sake karawa tsakanin Paris St- Germain da Manchester United

A kakar 2018/19 Paris St Germain sun hada a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar ta Champions League.

A gidan United wato Old Trafford aka fara karawar farko, inda PSG ta yi nasara da ci 2-0. A wasa na biyu kuwa a Faransa United ce ta doke PSG da ci 3-1 ta kai zagayen gaba.

Shin ko wannan fafatawar yaya za ta kaya?

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...