Champions League: Fafatawar Real Madrid da Ajax

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid za ta karbi bakuncin Ajax a wasa na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions Leageu da za su fafata a Santiago Bernabeu a ranar Talata.

A wasan farko da suka kara a gasar ranar 13 ga watan Fabrairu, Real ce ta doke Ajax da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a Netherlands.

Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Karim Benzema daga baya Ajax ta farke ta hannun Hakim Ziyech, daf da za a tashi daga karawar Real ta kara na biyu ta hannun Marco Asensio.

Sai dai kuma kyaftin din Madrid, Sergio Ramos ba zai buga fafatawar ba, sakamakon kar bar katin gargadi da gangan da ya yi, daga baya hukumar kwallon Turai ta ce ta dakatar da shi wasa biyu.

Ramos ya yi wa Kasper Dolberg na Ajax keta a minti na 89, wanda hakan yake nufin an dakatar da shi daga buga wasan gaba.

Dan wasan bayan Spain din ya shaida wa manema labarai cewa “zai yi karya idan ya ce bai nemi hakan da gangan ba”.

Hukumar Uefa ta yi bincike game da batun kuma ta hana shi buga karin wasa guda saboda ya nemi katin gargadi da gangan.

Bayan da Ramos ya karbi katin gargadin, hakan yana nufin ya rage yiwuwar kin buga wani babban wasa da ke gaba.

Sai dai saboda wannan hukunci na hukumar Uefa, idan Real Madrid ta kai matakin wasan gab da na karshe, Ramos ba zai buga wasan ba.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...