
Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya shirya tsaf domin tafiya kasar Ethiopia inda zai halarci babban taron kungiyar kasashen Afrika ta AU.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar ta ce Buhari zai bar Abuja a ranar Alhamis ya zuwa birnin Addis Ababa na Ethiopia.
Buhari zai halarci taron kungiyar AU karo na 36 wanda zai mayar da hankali kan yadda za a gaggauta aiwatar da yarjeniyar kasuwancin bai ɗaya a tsakanin ƙasashen Afrika da a kaiwa lakabi da AFCTA.
Har ila yau a yayin taron ana sa ran shugaban kasa Buhari zai halarci tarukan kungiyar ta AU kan zaman lafiya da tsaro, sauyin yanayi da kuma halin da dimakwardiya ke ciki a wasu ƙasashen Afrika ta yamma.