Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari’a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya.

Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus da tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, mai shari’a, Tanko Muhammad yayi saboda lalurar rashin lafiya.

A kwanakin baya ne wasu alkalai dake kotun suka zargi, mai shari’a, Tanko da tauye musu wasu hakkuna nasu da kuma almubazzaranci da kudaden kotun koli.

More from this stream

Recomended