Buhari ya kara jaddada matsayinsa kan batun tazarce | BBC Hausa

Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Fadar shugaban Najeriya ta sake jaddada cewa Shugaba Buhari ba ya da wata aniya ta zarcewa a matsayin shugaban kasa a karo na uku.

Wata sanarwa ta martani da mai magana da yawun shugaban ya fitar Mallam Garba Shehu ta yi watsi ne da abin da ya kira masu neman jan hankali a kafofin yada labarai kan ikirarin cewa shugaba Buhari na take-taken neman wa’adi na uku.

“Mun sake nanatawa: duk wani ikirari da ke nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai nemi wa’adi na uku karya ne,” in ji Garba Shehu.

Fitaccen lauyan nan me fafutukar kare hakkin dan adam a Najeriya, Femi Falana, ne ya fara cewa Buhari na neman wa’adi na uku ta hanyar sauya kundin tsarin mulki da zai ba shi damar tsawaita mulkin nasa.

Sanarwar ta ce Mr Falana na cin gajiyar ‘yancin fadin albarkacin baki da gwamnatin shugaba Buhari ta tabatarwa ‘yan kasar ne, amma baya ga haka babu wani yanayi ko matsi daga wasu masu ra’ayin yin tazarcen da zai sa shugaba Buhari ya amince da batun.

  • ‘Za mu tsananta rokon Buhari kan tazarce’
  • ‘Ina da hujjojin da ke nuna Buhari na neman wa’adi na uku’

Kuma game da batun da a ke ci gaba da yadawa, sanarwar ta ce, shugaba Buhari yana kara tunatarwa ga wadanda ko dai suna son wa’adi na uku ko kuma suna yada labarin karya saboda wasu bukatunsu cewa:

“Babu wani yanayi da har zai sa shugaba Buhari ya yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don neman karin wani wa’adi.

“Shugaba Buhari wa’adin mulkinsa na biyu kwai zai kammala da zai kawo karshe a 2023, sannan a yi zabe ba tare zama dan takara ba.”

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari dan dimukradiyya ne, yana kuma mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ba zai sabawa tanadin kundin tsarin mulki ba.

“Kuma Buhari ya kara nanata cewa ba zai nema ba kuma ba zai amince da wa’adi na uku ba.”

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...