Shugaban kasa, Muhammad Buhari yayi wata ganawa da gwamnonin jam’iyar APC a fadar Aso Rock.
Babau wata sanarwa da aka fitar kan dalilin taron sai dai wata majiya ta bayyana cewa taron baya rasa nasaba da zaben mutumin da zai yi wa jam’iyar APC takarar mataimakin shugaban kasa.
Tun bayan kammala zaben fitar da gwani da ya bawa tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu nasara ake ta kai ruwa rana musamman wajen ganin mutumin da ya dace ya yi masa mataimaki.
Wasu majiyoyi na kusa da Tinubu sun bayyana cewa hankalin sa yafi kwanciya da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin mataimaki.




