Buhari ya fi mazan Najeriya da yawa kwari, inji kungiyar kamfen Buhari

Kungiyar kamfen tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ‘yan Nijeriya kar su tsorata game da lafiyar shugaban kasar, domin yana cikin koshin lafiya, har ma ya fi da yawan mazajen Nijeriya kwari.

Mataimakin daraktan kungiyar, Arch Waziri Bulama ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a Abuja.

Bulama ya ce: “Ina ganin yadda Shugaban kasa yake kai-kawo a cikin wannan kamfe din ya nuna cewar ya fi da yawan mazajen kasar nan kwari. Wannan ne mutumin da a shekarunsa yake kai-kawo daga birni zuwa birni, sannan akalla yake zuwa birane biyu a kowacce ranar mako domin kaddamar da ayyuka, haduwa da shuwagabannin gargajiya da masu ruwa da tsaki, sannan kuma ya dawo domin ya fuskanci wasu ayyukan kasa da kuma wasu kungiyoyin a fadarsa ta Aso Rock.

Bayan nan kuma da safiyar washegarin ranar ya kuma shillawa wani garin ba tare da nuna alamar damuwa ko rauni ba. Shugaban kasa Buhari yana da lafiya da matukar kwarin da zai gabatar da ayyukansa, sannan kuma abun alfahari, yana bayar da irin shugabanci da lokacinsa da muke bukata a wannan kamfe din.”

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...