Buhari da Atiku sun sake sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Kasa da mako daya kafin babban zabe a Najeriya, manyan ‘yan takarar shugabancin kasar biyu watau Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar sun sa hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben da za ayi a ranar Asabar.

Kwamitin wanzar da zaman lafiya karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar na mulkin soji Abdulsalami Abubakar ne suka shirya taron.

‘Yan takarar biyu sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana da kuma kaucewa duk wani rikici ko hargitsi a lokacin zaben.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa kasarsu addu’a a daidai lokacin da ake fuskantar zaben da kuma kara tabbatar da hadin kai ga ‘yan kasar baki daya.

Ya kuma bayyana cewa zabe na da matukar amfani domin yana taimakawa wajen samar da zaman lafiya da kuma shirya kasa ta samu ci gaba.

A nasa bangaren, Atiku Abubakar ya yi kalamai irin na tsohon Shugaban Kasar Goodluck Jonathan inda Atikun ya bayyana cewa ba dan Najeriyar da ya kamata ya rasa ransa saboda burinsa na zama shugaban kasa.

Wannan ne karon farko da ‘yan takarar suka zauna wuri daya tun bayan da jam’iyyinsu suka fitar da su a matsayin ‘yan takarar shugabancin kasar.

Buhari dai na neman wa’adi na biyu karkashin jam’iyyar APC yayin da Atiku Abubakar wanda ya taba zama mataimakin shugaban kasa a Najeriyar ke neman shugabancin kasar karkashin jam’iyyar PDP.

Wannan ne karo na biyu da ake sa hannu a irin wannan yarjejeniya duk da cewa Atiku bai halarci yarjejeniyar farko da aka yi ba a shekarar da ta gabata.

Taron sa hannu a yarjejeniyar ya samu halartar tsaffin shuwagabannin kasashen Afirka da jakadun kasashe daban-daban da kuma masu sa ido a harkar zabe.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...