Wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki kan ayarin motocin da ke dauke da kayayyaki da fasinjoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, inda suka kashe mutane biyar tare da sace mata bakwai.
An kai harin ne ranar Alhamis kan ayarin motocin jami’an tsaro da ke dauke da manyan motoci kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru a karamar hukumar da misalin karfe 2:30 na rana.
Wata majiya mai tushe da ke tafiya a kan hanyar Maiduguri zuwa Bama zuwa Banki mai suna Babagana Kaumi, ta tabbatarta da harin: “An yi wa ayarin fasinjoji da motocin kaya kwanton bauna a kusa da Banki.”