Boko Haram: Shin karshen kungiyar ya zo ne?

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya sun shafe shekaru suna yaƙi da Boko Haram a Najeriya

Ana ci gaba da samun karuwar mayakan Boko Haram da ke tuba da mika wuya kuma ake karbarsu cikin al’umma a jihar Borno.

Fadar Shehun Borno ta gudanar da wani taro a ranar Talata kan fadakar da al’ummar Borno da wayar musu da kai – su rungumi tsofaffin ‘yan Boko Haram da suka ajiye makamai suka mika wuya ga gwamnati.

An gudanar da taron ne a fadar Shehun Borno da hadin gwiwar hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP da UNICEF don wayar da kan jama’ar jihar su karbi tubabbun mayakan da suka baro daji.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce sama da ƴan Boko Haram 8,000 suka miƙa wuya zuwa yanzu.

Babban Kwamandan runduna ta bakwai Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, ya ce sun mika wuya ne daga maɓuyarsu a dajin Sambisa, da kuma sauran inda suke ɓuya.

A cewar Kwamandan, miƙa wuya da tubabbun ƴan Boko Haram ke yi abin farin ciki ne, yana mai cewa yawan luguden wuta da ake masu ne dalilin tubarsu.

Kwamishina yada labarai na Bornon Baba Ƙura Abba Jato ya ce mafi yawan tubabbun mata ne da ƙananan yara. Akwai kuma waɗanda aka tilasta wa shiga Boko Haram da kuma waɗanda a baya suka shiga ƙungiyar da ta addabi Najeriya da maƙwabta sama da shekara 10.

Ya ce a yanzu haka an ajiye su a sansanoni biyar karkashin kulawar gwamnatin jiha, kuma ana fata jama’a za su karɓe su bayan an gama tantance su an ba su horon da ya dace.

Me tuban Boko Haram ke nufi?

Kwamishina Baba Kura Jato ya ce addu’ar da aka jima ana yi ce ta amsu, “shi ya sa Allah ya karkato da hankalinsu suka tuba.”

A yayin da waɗannan mayaƙa suke miƙa wuya an yi ta bayar da rahotannin yadda lamarin ya jefa shugabannin jihar Borno cikin tsaka mai wuya kuma ya sa masu sharhi suna yin kira da makukunta su yi kaffa-kaffa kan karbarsu.

A gefe guda, ana ganin miƙa wuyan na ƴan Boko Haram a matsayin wata alama ta kawo ƙarshen yaƙi da ƙungiyar mai da’awar kafa Daular Islamiya a Najeriya ta shafe shekaru 12 tana yi.

Sai dai kuma a wani bangaren ana fargabar hakan ka iya zama kitso da kwarkwata idan aka yi la’akari da yadda wasu da suka taba tuba suka koma fagen daga.

A wata sanarwa, gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya taɓa cewa karɓar ƴan Boko Haram da suka tuba yana tattare da hatsarin fusata waɗanda rikicin ya shafa kamar yadda tubabbun ƴan Boko Haram za su iya shiga ISWAP idan aka ki karɓarsu.

Don haka hukumomi na ganin babu wani zabi dole a karbe su cikin al’umma don fargabar kada susake komawa inda suka fito.

Mahukunta da wasu daga cikin gwamnonin shiyar arewa maso gabashin Najeriya na kira ga al`umma da ta yi maraba da miƙa-wuyan da mayaƙan Boko Haram ke yi, maimakon yanke-ƙauna da wasu ke yi gama da sahihancin tubarsu.

Masu sharhi kan tsaro a Najeriya na ganin watakila, mika wuyan, na da nasaba da murkushe su da ake yi a yanzu da kuma mutuwar shugabansu Abubakar Shekau.

Masanin harkokin tsaro kuma jami’i a Cibiyar Bincike ta Tony Blair da ke Burtaniya, Barista Bulama Bukarti ya shaidawa BBC cewa wannna kungiya ce da ta soma tun lokacin jagoranta Muhammadu Yusuf.

“Burinta shi ne rungumar ayyukan al-Qaeda kuma ta hakan ya hada mambobin wannan kungiyar da niyyar mamaye yankunan Sahel kan akidunsu,”

“Akwai kuma masu cewa watakila tuban mayakan ya kawo karshen ayyaukanta, ganin cewa karfin mayakan na raguwa da kuma raguwar kai hare-harensu.,” in ji shi.

Bayan mutuwar wanda ya kafa ta a hannun ƴan sanda a shekarar 2009, Shekau ya jagoranci sauya ƙungiyar daga wata ƙungiya ta bayan fage zuwa mai kai munanan hare-hare da ta mamaye arewa maso gabashin Najeriya da ƙasashen tafkin Chadi.

Akidunsa na da tsauri saboda bai ragawa kowa ba kama daga mata da kananan yara, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, a zamaninsa babu wanda ya tsira, a cewar Bulama Bukarti

A shekara ta 2014 Shekau ya bayyana mubaya’a ga mayakan IS da ke ayyukan ta’addanci a gabas ta tsakiya.

Boko Haram a yanzu na aiki tare da wannan mayakan, kuma Shekau ya gina mabiyansa ne bisa tsattsauran ra’ayi.

Sai dai kuma an kai wani matsayi da ayyukan Shekau ya rinka ɓatawa mabiyansa rai da ke ganin ya fiye tsauri.

An ta samun korafe-korafe tsakanin mayakan, musamman wadanda suka dage ala tilas ya bar matsayinsa, wannan rikici tsakanin mayakan ya raba kawunansu, in ji Burkati.

An kai ga kafa wani ɓangaren kungiyar da Abu musa al-Barnawi ke jagoranta, mai suna ISWAP. Wannan ya kai ga an soma samun yaki tsakanin bangarori biyu inda suka dinga yaki da kashe junansu.

Bulama ya ce shugaban Iswap Abu Musab al-Barnawi, ya ce “ya kashe kansa nan take ta hanyar kunna abin fashewa”.

Mayakan Iswap sun gano shugaban ƙungiyar Boko Haram ɗin ne kuma suka ba shi damar tuba ya koma cikinsu, a cewar al-Barnawi.

“Shekau ya gwammaci ya tozarta a lahira da ya tozarta a duniya,” a cewarsa.

Karshen yakin Boko Haram ko akasain haka

Har yanzu dai babu tabbacin mika wuyan mayakan zai yanke hukunci kawo karshen mayakan ko yakin da ake yi da su. Amma duk da haka wata gagarumar nasara ce a yaki da mayakan kamar yadda masana ke cewa.

A baya wasu na hasashen cewa mutuwar Shekau na iya kawo ƙarshen mummunar hamayyar da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu, kuma wannan zai ba Iswap damar janye hankalin mayaƙan Boko Haram amma wasu na cewa za su ci gaba da riƙe aƙidar Shekau.

Haka kuma masana na cewa wannan ita ce damar karshe ga sojoji su yi amfani da dabarun yaki wajen kakkabe su baki daya, ganin a koda yaushe ana samun tururuwar mayaka da ke tuba.

Ko da yake a gefe guda akwai fargaba da masu ganin cewa akwai bukatar yin takatsantsan kar garin neman gira a rasa ido.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...