Boko Haram ba ta kai hari a Barikin Maimalari ba

@

Rundunar sojin Najerya ta karyata labarun da ke yawo a shafukan zumunta cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a barikin Maimalari da ke Maiduguri ranar Asabar 29 ga Fabrairu, 2020.

Labaran na cewa sojoji sun kama mayakan Boko Haram da suka yi shigar burtu a matsayin jami’an Majalisar Dinkin Duniya a harin da suka yi yunkurin kai wa barikin soji mafi girma a jihar Borno.

An ga hotunan wasu mutane da sojoji suka tsare sanye da kaya da motoci irin na ma’aikatan MDD a hotuna da bidiyon da aka yi ta yadawa.

Amma a sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta bukaci jama’a da su yi watsi da labarin. Rundunar ta yi bayani cewa hotunan an dauke su ne a lokacin wani horo na musamman da aka yi tsakanin jami’an MDD da sojojin rundunar Operation Lafiya Dole.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Sagir Musa, ya kara da cewa babu wata barazanar tsaro da aka samu a barikin Maimalari ko garin Maiduguri a ranar kamar yada labarin kanzar kuregen ke ikirari.

Sanarwar ta kuma ba wa jama’ar jihar tabbacin samun tsaro domin harkokinsu da harkokin ba tare da fargaba ba, sannan ta shawarce su su rika tantance labaran da suke samu ta shafukan zumunta.

Mene ne labaran karya?

Labaran karya sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.

Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.

Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.

A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

Alkalumma sun ce kimanin mutum miliyan 26 da suke amfani da shafin sada zumunta na Facebook a Najeriya, wannan dalili da kuma karuwar masu amfani da wayoyin hannu masu komai-da-ruwanka, na taimakawa wajen saurin yada jita-jita a kafafan sada zumunta.

Hotuna na karya da ake yadawa a kafafan sada zumunta wanda mutane ke ikirarin rikici ne a tsakanin al’umma, na kara haifar da zaman dar-dar a Najeriya.

Hakan na faru ne kwana uku da barkewar wani mummunan rikici tsakanin wasu da ake zargin makiyaya ne da kuma manoma, lamarin da haifar da asarar rayukan mutane fiye da 200 a jihar Filato.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar cigaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokacin da ake tunkarar zaban shugaban kasa a badi.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana’ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa. Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu. Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na’urar da aka yi amfani da ita. Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu ya ke.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...