Bene ya sake ruftawa da mutane a Ibadan

Wani ginin bene ya ruguzo a yankin Bode dake Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Wata majiya dake yankin ta shedawa jaridar The Cable cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe 05:50 na yamma.

Ruftawar ginin na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan ruftawar wani ginin bene dake dauke da makarantar firamare a yankin Itafaji a jihar Lagos inda akalla mutane 20 suka rasa rayukansu.

Ana tsammanin cewa mutane da dama sun makale a cikin ginin benen.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Oyo,ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa ana cigaba da aikin ceto a wurin da lamarin yafaru.

“Abin da yafi muhimmanci a yanzu shine kawar da baraguzan ginin, domin ceto mutanen da suka makale bayannan kuma sai tantance wadanda abin ya rutsa da su,”ya ce.

More News

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da suka yi bacci a lokacin da suke tsare da mutanen da suka sace

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane bayan da suka buge da sharar bacci a lokacin da suke tsare...