Batun Rashin Kammalar Zabe Bai Da Muhalli – Tanbuwal

Aminu Tambuwal, Gwamnan jahar Sakkwato kuma dan takarar gwamnan jahar a karkashin jam’iyyar PDP, ya kira taron manema labarai jiya a fadar gwamnatin jahar, inda ya ce a yayin da hukumar zaben kan alakanta ayyana rashin kammalar zabe da tanajin dokar zabe, gwamna Tambuwal ya ce sun dubi kundin tsarin mulki da kuma tanajin dokar zabe ba su wannan tanaji ba. Ya kara da cewa hukumar zaben ba ta bayyana masu runhunan zaben da aka soke zabukansu da kuma dalilan da su ka sa aka soke ba.

Gwamna Tambuwal ya amsa cewa akwai dalilan da kan sa a soke zabe ta yadda ma na za a sake yi ba; akwai kuma dalilan da kan sa a soke amma kuma a sake wani sabo. Ya ce to amma hukumar INEC ba ta alakanta daya daga cikin irin wadannan yanayoyi da ayyana zaben jahar Sokoto a matsayin mara kammala da ta yi ba.

Gwamna Tambuwal ya ce ta na yiwuwa su ruga kotu su kalubalanci ayyana zaben a matsayin mara kammala. Ya kuma yi nuni da cewa akasarin jahohin da aka ayyana zabensu a matsayin marasa kammala ‘yan takarar PDP ne ke kan gaba. Sannan ya yi hanunka mai sanda ga jami’an hukumar INEC da cewa idon duniya na kansu.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...