Barcelona za ta gabatar da Xavi gaban magoya baya ran Litinin

Xavi Hernandez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Xavi ya buga wa Barcelona tamaula tsakanin 1998 zuwa 2015

Barcelona za ta gabatar da Xavi Hernandez a matakin sabon locinta a gaban ‘yan kallo ranar Litinin.

Kungiyar ta shirya bikin gabatar da tsohon dan wasanta a matakin mai horarwa a filin wasa na Nou Camp.

Daga nan ne zai gana da ‘yan jarida, bayan da ya maye gurbin Ronald Koeman, wanda ta sallama daga aikin, shima tsohon dan wasan Barcelona ne da ya taka rawar gani.

Tuni dai Xavi ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2024.

Dan kasar Sifaniya mai shekara 41 ya fara horar da Al Sadd tun daga 2019, wanda ya amince ya karbi aikin jan ragamar Barcelona ranar Juma’a.

Barcelona ta sanar cewa Xavi zai horar da kungiyar zuwa karshen kakar bana daga nan ya kara kaka biyu a gaba.

Xavi, wanda ya yi wa Barca karawa 767 a kungiyar ya lashe kofi 25 a shekara 17 da ya yi a Camp Nou,

Daga nan ya koma Al Sadd a matakin dan wasa a 2015, sannan ya zama kocinta.

Ya kuma karbi aikin horar da kungiyar Qatar a 2019, wanda ya lashe kofin lik din a bara, kuma kungiyar ta yi karawa 36 a Lik din ba a doke ta ba.

Tun bayan da Barcelona ta kori Ronald Koeman ranar 27 ga watan Oktoba ake alakanta shi da aikin.

Barcelona tana ta tara a teburin La Liga, bayan da ta ci kwallo uku ranar Asabar a gidan Celta daga baya aka farke ta tashi 3-3 a wasan mako na 13 a gasar Sifaniyar.

Yadda aka tsara gabatar da Xavi ranar Litinin:

11.30 na safe za a buge kofofin filin wasa na Camp Nou.

1.00 na rana za a gabatar da Xavi Hernandez a matakin sabon kocin kungiyan Barcelona a tsakiyar filin Camp Nou.

1.30 na rana Xavi Hernandez zai yi hira da ‘yan jarida

More News

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...