Barcelona ta kara shiga tsaka mai wuya

Sergio Aguero

Asalin hoton, Getty Images

Kocin rikon kwarya Sergi Barjuan ya fara jan ragamar Barcelona da tashi 1-1 da Deportivo Alaves a Nou Camp ranar Asabar a gasar La Liga.

Karon farko da kungiyar ta buga wasa, bayan da ta kori Ronald Koeman ranar Laraba, wanda ya fara jan ragama cikin Agustan 2020.
A karawar ta ranar Asabar fitattuun ‘yan wasanta biyu sun ji rauni da hakan ka iya kara jefa kungiyar cikin matsi a fafatawar da ke gabanta.
Sergio Aguero ya fita daga karawar ranar Asabar, bayan da jiri ke damunsa da kasa nunfashi da ciwon kafata, wanda aka garzaya da shi asibiti.

Wasa na biyar kenan da dan kwallon tawagar Argentina ya buga wa Barcelona a bana, bayan da ya yi jinya tun kan fara kakar nan.

QAna kuma tsaka da wasa ne Gerard Pique ya ji rauni, inda Clement Lenglet ya canje shi.
Cikin wadanda ke jinya a Barcelona kawo yyanzu sun hada da Frenkie de Jong da Ansu Fati da kuma Martin Braithwaite.
Sauran sun hada da Sergi Roberto da Pedri da Ronald Araujo da kuma Ousmane Dembele ga kuma Aguero da Pigue.
Kawo yanzu kungiyar Camp Nou ta fice daga gurbin da kungiyoyin Sifaniya ke wakiltarta a gasar Zakarun Turai.
Barcelona mai kwantan wasa tana mataki na tara a teburin La Liga da maki 16 da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid ta daya.
Ranar Talata Barcelona za ta fafata da Dynamo Kiev a gasar Champions League.

(BBC Hausa)

More News

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da suka yi bacci a lokacin da suke tsare da mutanen da suka sace

Jami'an Æ´an sanda sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane bayan da suka buge da sharar bacci a lokacin da suke tsare...