Barayin ƙarfen digar jirgin ƙasa sun fada hannun jami’an tsaron Civil Defenc

Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC sun tare wasu manyan motocin kaya guda biyu dake dauke da karfen digar jirgi a yankin Ooloru dake jihar Kwara.

Kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kwara, Umar Mohammed ya fadawa yan jarida a Ilorin ranar Laraba cewa an kama mutane shida dake tare da motocin biyu.

Ya kuma kara da cewa mutanen da aka kama sun tawo ne daga kauyen Jagundi a karamar hukumar Kafanchan ta jihar Kaduna.

Kwamandan ya ce a yayin kamen mutane biyu sun samu nasarar tserewa amma ya ci alwashin za su shiga hannu nan ba dadewa ba.

Tuni hukumar ta nemi umarnin kotu domin cigaba da tsare motocin da kayan ke ciki har zuwa lokacin da kotu za ta zartar da hukunci kan batun.

Da ya daga cikin mutanen da aka kama Yunusa Bello ya ce bai san kayan na sata ba ne kuma an dauke shi kwangilar tuka motar ne da zummar za a biya shi miliyan daya.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...