‘Baraka ta kunno kai a fadar Shugaba Buhari kan tsaro’ | BBC Hausa

Kyari da Monguno

Baraka ta kunno kai a fadar shugaban Najeriya, bayan mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya zargi shugaban ma`aikata a fadar, Abba Kyari da yin shisshigi a cikin al`amuran da suka shafi tsaro.

Manjo-Janar Monguno mai ritaya ya ce katsalandan din da Abba Kyari ke yi a aikinsa ya takaita nasarorin da ake samu a kokarin inganta tsaro a Najeriya.

Babu dai wani martani daga bangaren shugaban ma’aikatan.

Manjo-Janar Monguno ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasikar da ya aike wa hafsoshin tsaron kasar tun a watan Disambar 2019.

An dai tsegunta wa jaridar intanet ta Premium Times, cewa Abba Kyari yana katsalandan a cikin harkokin tsaro ta hanyar ba wa hafsoshin tsaro umarni.

A cewar Monguno, a wani lokaci Abba Kyari kan yi gaban-kansa wajen jagorantar zama da hafsoshin tsaron da kuma wasu muhimman mutane irin jakadun wasu kasashe a Najeriya ba tare da sanin Shugaba Buhari ba.

Mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkar tsaron ya ce irin wannan zakewa da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati ke yi ta saba wa ka’ida, saboda ba huruminsa ba ne.

Ya kara da cewa irin wannan kutsen da yake yi wa aikin wasu, shi ya yi cikas ga fadi-tashin da gwamnatin Najeriyar ke yi wajen inganta tsaro ba ya tsinana wani abin a zo a gani.

Gargadi ga hafsoshin tsaro

Manjo-janar Monguno ya gargadi hafsoshin tsaron da su guji daukar umurni daga Malam Abba Kyari.

Har yanzu fadar shugaban kasa ta yi gum da bakinta a kan wannan batu.

Sai dai jam’iyyar PDP mai hamayya ta yi ikirarin cewa wannan takaddama da ake yi tsakanin manyan jami’an gwamnatin biyu ta nuna cewa Shugaba Buhari ya kaurace wa aikinsa na gudanar da mulki.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, PDP, ta ce zargin da mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha’anin tsaro ya yi ya nuna abin da ta dade tana fada cewa shugaban kasar bai san abubuwan da ke wakana a gwamnatinsa ba.

“Bayan wannan kalami da mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro ya yi, PDP tana jaddada kiran ta cewa kada shugaban kasa ya bata lokaci wajen sauka daga kan mukaminsa na shugaban kasa, domin a fili take cewa ba zai iya gudanar da aiki ba,” in ji PDP.

PDP ta ce tana bai wa harkokin tsaro matukar muhimmanci a bangaren mulki, daga nan sai walwalar jama’a kuma tun da Shugaba Buhari ya gaza aiwatar da wannan nauyi bata ga dalilin ci gaba da zamansa a kan mulki ba.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...