Connect with us

Hausa

Bankin duniya ya nemi tallafin G7 | Labarai

Published

on

Kawo yanzu dai cutar corona ta kashe mutane miliyan 3 da dubu 700, daga cikin sama da miliyan 170 da suka kamu. Hadakar cibiyar nazarin annoba ta kasa da kasa ta ce, tsakanin shekara ta 1918 zuwa 1919 annobar murar H1N1, ta yi sanadiyar rayukan mutane miliyan 50, da ke wakiltar kaso daya daga cikin ukun al’ummar duniya.

To sai dai a yayin da lamura suka fara daidaituwa a kasashe kamar Amurka da Birtaniya godiya ga allurar rigakafin na COVID, har yanzu akwai kasashe masu yawa da basu da sukunin samun alluran da suke bukata.

Richard Hatchett da ke jagorantar shirin tallafin allurar ga kasashe matalauta na MDD da ake kira COVAX, ya bada misalin Peru, a matsayin kasar da lamura suka lalace na karuwar yawan wadanda ke kamuwa da corona.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending