Bala’i: Tsadar rayuwa ta sa wani ya cinna wa kansa wuta

Wani mutumi a birnin Mombasa na kasar Kenya ya cinna wa kansa wuta saboda tsananin tsadar rayuwa.

Da ma dai mutumin ya ce yana zanga-zanga kan tsadar rayuwar, sannan daga baya ya cinna wa kansa wuta a ranar Alhamis da tsakar rana.

A cewar wani rahoton BBC Hausa, ya hau kan wani wurin mutum-mutumi da ke tsakiyar wani shatale-tale kafin cinna wutar.

Wani bidiyo da ya yi yawo sosai a shafukan zumunta, ya nuna mutumin riƙe da tutar ƙasar ta Kenya yana ihu, inda nan da nan kawai sai aka ga wuta ta turnuke wajen.

More from this stream

Recomended