Babu shirin ƙara farashin Man Fetu, inji IPMAN

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN ta karyata ikirarin da ake yi na cewa kungiyar na da niyyar kara farashin man fetur zuwa Naira 700 kan kowace lita.

Dele Tajudeen, Shugaban IPMAN shiyyar Kudu Maso Yamma ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi ranar Juma’a a Ibadan, kamar yadda NAN ta ruwaito.

Ya kuma fada wa ‘yan Najeriya da kada su rika saka kansu a cikin damuwa, su yi watsi da jita-jitar.

An ambato shi yana cewa, “Ba yadda za a yi farashin ya kai N700 kamar yadda muke magana, domin ko da FX N700 ne ko N800, wannan ba abin da zai iya daukar farashin man fetur daga N500 zuwa N700 ba ne.”

Ya kuma yabawa shugaban kasar kan cire tallafin man fetur, inda ya kara da cewa abu ne da ya kamata a yi shi tun ba yau ba.

More from this stream

Recomended